Labarai
Har yanzu Atiku dan jam’iyyar PDP ne- Ibrahim Dankwambo

Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa, Ibrahim Dankwambo, ya ce, har yanzu tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abububakar, dan jam’iyyar PDP ne duk da komawar da yayi jam’iyyar hadaka ta ADC.
Da ya ke jawabi yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana na jam’iyyar a Gombe a daren jiya Lahadi, Dankwambo ya bayyana Atiku a matsayin jagora wanda darajar sa ba zata taba canjawa ba.
Dankwambo ya kuma yaba da irin gudunmawar da shugabannin arewa ke bayarwa, musamman mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo.
You must be logged in to post a comment Login