Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Har yanzu muna laluben inda aka ɓoye tsohon shugaban NPA a Kano – Ƴan sanda

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, har yanzu tana ci gaba da binciken inda aka ɓoye tsohon shugaban hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta ƙasar nan Alhaji Bashir Abdullahi.

Mai Magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a zantawar sa da Freedom Radio.

Ya ce “Tun a ranar 3 ga watan Nuwamba ne bayan da muka samu rahoton sace shi a kauyen Dan sitti da ke garin Gomo a ƙaramar hukumar Sumaila a Kano, muka baza jami’an mu na rundunar kan-kace-kwabo domin nemo inda aka ɓoye shi”.

“Daga binciken mu na farko mun gano cewa Alhaji Bashir Abdullahi ya bar cikin gari ya koma gonar sa da zama tsawon sati biyu, sai dai za mu ci gaba da bincike don gano gaskiyar lamari”.

Rundunar ta gargaɗi al’umma da su riƙa kai bayanan duk wani motsi da basu gamsu da shi ba.

Idan za a iya tunawa, tun a ranar 3 ga watan Nuwamba ne aka sace Alhaji Bashir Abdullahi a kan hanyar sa ta dawowa daga gonar sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!