Labarai
Hare-haren Boko Haram ne ya hana Jonathan cire tallafin mai – Sarki Sunusi II

Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II kuma tsoho gwamnan Babban Bankin kasa CBN, ya bayyana cewa tsoron hare-haren Boko Haram ne ya sa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dakatar da shirin cire tallafin man fetur a shekarar 2012.
Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Talata, a taron Oxford Global Think Tank Leadership da ƙaddamar da wani littafi, Sanusi ya ce ba zanga-zangar jama’a ba ce ta sanya gwamnatin Jonathan ta ja da baya, sai dai bayanan sirri da gwamnati ta samu kan yiwuwar kai hare-hare a wuraren da masu zanga-zanga suka taru.
A cewar Sarkin, gwamnatin wancan lokaci ta fi mayar da hankali wajen kare rayukan ‘yan kasa, musamman ganin cewa kungiyar Boko Haram na cikin mafi girman tashin hankali a Arewa maso Gabas a lokacin.
You must be logged in to post a comment Login