Labarai
Harin Masallaci a Borno ya hallaka mutane 5

Wani mummunan tashin bam ya auku a wani masallaci dake kasuwar Gamboru a cikin birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a yammacin jiya laraba, inda har yanzu ba a tabbatar da adadin waɗanda suka rasu ko suka jikkata ba, sai dai rahotanni na nuna cewa mutane da dama ne suka jikkata ko suka rasa rayukansu.
Rahotanni sun ce tune an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban domin samun kulawar gaggawa, yayin da jami’an tsaro suka kasance a wajen.
Sai dai daga bisani gwamnatin jihar ta fitar da rahoton cewa, mutane 5 ne suka rasu sakamakon harin, yayin da 35 kuma suka jikkata.
You must be logged in to post a comment Login