Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida – El-rufa’i

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da harin yan bindiga da yayi sanadiyyar mutuwar mutane shida tare da jikkata mutum guda a kananan hukumomin Igabi da Kauru da ke jihar.

 

Kwamishinan Tsaro na cikin gida Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Talata.

 

Aruwan ya ce an kashe mutane shida a wasu hare-haren yan bindiga da ya faru a kananan hukumomin Igabi da Kauru, kamar yadda hukumomin tsaro suka bayyana.

 

A  cewar sa a karamar hukumar Igabi yan fashin sun tare hanyar Birnin Yero-Tami, kuma sun kashe mutum daya tare da jikkata mutum daya kuma yanzu haka yana karbar magani a asibiti.

 

Aruwan ya kuma ce, a kauyen Gwada da ke karamar hukumar Igabi wani harin da ‘yan bindiga suka kai ya yi sanadin mutuwar mutum biyu, sai kuma wani harin da yan bindigar suka mamaye Ungwan Kure, suka kashe mazauna yankin biyu.

 

Hakazalika, ‘yan bindigar sun kai hari kan matsugunan Amawan Dadi Rugan Jauru da ke karamar hukumar Kauru kuma tare da harbe mutum guda.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!