Labarai
Harkokin tsaron Najeriya na ƙara tabarbarewa- Rahoto

Wani sabon rahoto ya bayyana cewa halin tsaron Najeriya ya ƙara tabarbarewa a cikin shekara guda da ta gabata, sakamakon hare-hare da aka rika kai wa ofisoshin ‘yan sanda, wuraren bincike a jihohi daban-daban na ƙasar.
Rahoton ya ce hare-hare sun yi sanadin halaka jami’an ‘yan sanda da dama, da aka kona ofisoshi, tare da kwace makamai, kana aka saki wadan da ake tsare da su.
Jaridar Daily Trust, ta ruwaito cewa, akalla jami’an ‘yan sanda 45 ne suka rasa rayukan su a cikin shekara guda sakamakon hare-hare kan ofisoshin ‘yan sanda, wuraren bincike a Borno, Kwara, Enugu, Kano, Jigawa, Bauchi, Plateau, Kogi, Taraba, Benue, Zamfara, Niger, Edo, Kaduna da Oyo.
You must be logged in to post a comment Login