Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan bindiga sun kai hari a kauyuka 2 da ke Katsina

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da wani hari da aka kai kauyukan Kanawa da Runka a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar SP Gambo Isah ne ya tabbatar da hakan, har ma ya ce, harin ramuwar gayya ce sakamakon yadda mazauna kauyen Kanawa suka kashe wani mutum mai suna Mani Doro.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa mazauna yankin sun shaida cewa ‘yan bindigar sun kai hari kauyukan Kanawa da Runka tare da hallaka mutane shida a ranar Lahadin da ta gabata, lamarin da ya tarwatsa al’ummar yankunan.

Maharan sun shiga kauyukan akan ababen hawa sama da sittin, abinda ya haifar da jikkatar mutane da dama baya ga rasa rayukan mutane shida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!