Connect with us

Labaran Kano

Hisbah ta kama mai yiwa mata kunshi

Published

on

Hukumar Hisbah ta karamar hukumar Fagge a nan Kano ta cafke wani mutum da ake zargi da yiwa mata kwalliya da kunshi

Ana zargin mutumin da yiwa mata zanen kunshin fulawa a sassa daban-daban na jikin su.

Wakilin mu Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito mana cewa dakarun Hisbah masu aiki na musamman a karamar hukumar Fagge su ne suka samu nasarar cafke mutumin a yankin Sabon Gari dake nan Kano.

Har ila yau, wakilin namu yayi kokarin jin ta bakin wanda ake zargin amma hakan ya ci tura.

Dan Hisbah yayi karar hukumar Hisbah a Kano

Hukumar Hisbah ta Kano ta cimma yarjejeniyar aiki da KAROTA

Da dumi-dumi: Hisbah ta janye dokar hana cakuda maza da mata

Shi ma da yake shedawa Freedom Rediyo, Kwamandan hukumar Hisbah ta Fagge Ustaz Jamilu Yusuf Muhammad Fagge cewa, yanzu haka suna cigaba da bincike domin daukar matakin da ya dace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,403 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!