Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hisbah ta kama matashin da ke shunawa mata gabansa a Kano

Published

on

Hukumar Hisbah a Kano ta tsare wani matashi bisa zargin shunawa mata gabansa tsirara a unguwar Na’ibawa Rimin Hamza.

Tun da farko dai matan auren unguwar ne suka yi ƙorafi ga jami’an sintirin yankin.

Matan sun ce, matashin na kwaye al’aurarsa idan ya ga mata sun zo wucewa.

Matashin ya shaidawa Freedom Radio cewa, yana aikata hakan ne a lokacin da ya shiga wani sauyin yanayi.

Mahaifiyar matashin ta ce, bata taɓa sanin yana aikata hakan ba, amma ita ma zata ɗauki mataki a kai.

Ustaz Muhammad Cheɗi shi ne shugaban sashen gudanarwa na Hisbah ta Kano ya ce, za su ci gaba da tsare matashin har zuwa lokacin kammala bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!