Labarai
NEMA ta jagoranci aikin ceto bayan ambaliyar ruwa data afkawa ƙauyuka 13 a Adamawa

Hukumar ba da agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) reshen Yola da ke jihar Adamawa ta jagoranci aikin ceto bayan ambaliyar ruwa data afkawa ƙauyuka 13, da ke cikin ƙananan hukumomin Jihar.
Shugaban ayyukan hukumar ta NEMA a Yola, Ladan Ayuba, ya ce tawagar gaggawa daga hukumar tare da hadin gwiwa da ta jihar ADSEMA, da jami’an kashe gobara na jiha da na tarayya tare da masu aikin sa-kai sun shiga yankunan domin ceto jama’ar da ambaliyar ta rutsa da su.
Ladan Ayuba ya kara da cewa an kwashe mata da yara da tsofaffi da masu nakasa daga yankunan da ke cikin haɗari zuwa sansanonin wucin-gadi da wuraren da suka dace. Inda kuma ake cigaba da bincike don gano girman illar ambaliyar, da asarar dukiya da gine-gine da aka samu, da kuma duba agajin da ake bukata a yankunan.
Sai dai kuma ya tabbatar da cewa, babu wanda ya rasa ransa sakamakon ambaliyar ruw
You must be logged in to post a comment Login