Labarai
Hukumar Consumer ta kama gurɓataccen manja a Kano
Hukumar kare haƙƙin masu sayen kaya ta jihar Kano da haɗin gwiwar hukumar KAROTA sun kama wasu tarin gurɓatattun kayayyakin sarrafa abinci da magunguna a jiya Talata.
An kama kayayyakin a wani sumame da jami’an hukumomin suka kai kasuwannin Singa da Sabon Gari da Kasuwar Kurmi da kuma Kasuwar Rimi.
Mai taimakawa Gwamnan Kano kan ayyukan hukumar KAROTA Malam Nasir Usman Na’ibawa ya yiwa Freedom Radio karin bayani a kai.
Ya ce, kayyakin da aka kama sun haɗa da hodar da ake haɗa madara da manja.
Sannan an kama gurɓatattun magunguna waɗanda ake amfani da su a Islamic Chemist.
Ya ce, tuni aka shiga faɗaɗa bincike a kai, ganin yadda ake ƙara bankaɗo kayayyakin da tunani bai kai kan su ba.
Hotunan kayayyakin da aka kama:
You must be logged in to post a comment Login