Labarai
Hukumar ECOWAS tace za ta hada kai da kungiyoyin wajen dakile ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasashen Afirka
Hukumar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS tace zata hada kai da kungiyoyin kishin al’umma domin dakile matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi a wasu kasashen yammacin afirka shida.
Da yake jawabi yayin wani taron karawa juna sani, mai take hanyoyin da za’a bi wajen dakile matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi, jami’in da ke lura da sashen yaki da matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi na hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa Daniel Amankwaah ya ce matsalar safarar miyagun kwayoti hadi da ta’ammali da su na daga cikin shirin cigaban muradan karni da za’ayi kokarin dakile su daga nan 2030
Ya bayyana cewa hadin gwiwar dakile wannan matsalar tare da kungiyoyin kishin al’umma zai taimaka gaya wajen dakile wannan annoba, inda ya lura da cewa ba za’a samu nasarar kakkabe wannan matsala ba, ba tare da tallafin bangarori masu zaman kan su, musamman ma kungiyoyin kishin al’umma.
Babban jami’in majalisar dinkin duniya mai kula da sashen matsalar miyagun kwayyi da makamantan su, a yankin yammacin afirka da kuma afirka ta tsakiya Cheikh Toure yace an shirya taron karawa juna sanin ne domin lalubo hanyoyin da za’a bi wajen magance matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin matasa da kananan kara, musamman ma mata.
Kasashen da hukumar ta ECOWAS zata aiwatar da aikin sun hadar da kasar Burkina Faso da Cape Verde da Laberiya da Maurtaniya da Sierra Leone da kuma kasar Togo.