Labarai
Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu manyan jami’an hukumar INEC a babbar kotun Lagos
Hukumar EFCC ta yi holin wasu manyan jami’an hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC na jihar Ogun a gaban babbar kotun jihar Legas saboda zargin sama da fadi da kudi kimanin Naira miliyan 179.
Hukumar dai ta EFCC ta yi holinYemi Akinwomi da Dickson Atiba da kuma Ogunmodedeoladayo a gaban Mai Shariha Sule Hassan na zargin hada baki domin amfana da kudaden da bai halatta a agaresu ba tare da bin hanyar da ta ba dace ba na karabar kudade.
Wadanda ake zargin dai sun karbi kudaden ne daga Bankuna da dama masu zaman kansu a daf da lokacin da za a fara zaben shekarar 2015.
sai dai dukkanin su snu musanta zargin da ake yi musu a zaman kotun.
Daga nan mai Shariah Sule Hassan ya dage cigaba da sauraranshariar har sai ranar 6 ga watan Augusta mai kamawa domin neman beli.
An daga zaman ne dai bayan jami’an hukumar zaben ta kasa mai zaman kanta sun musanta zargin da aka yi musu sannan kotun ta bayar da Umarnin da akai jami’an gidan Yari har sai ranar da za’a saurare su domin bayar da beli.