Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu manyan jami’an hukumar INEC a babbar kotun Lagos

Published

on

Hukumar EFCC ta yi holin wasu manyan jami’an hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC na jihar Ogun a gaban babbar kotun jihar Legas saboda zargin sama da fadi da kudi kimanin Naira miliyan 179.

Hukumar dai ta EFCC ta yi holinYemi Akinwomi da Dickson Atiba da kuma Ogunmodedeoladayo a gaban Mai Shariha Sule Hassan na zargin hada baki domin amfana da kudaden da bai halatta a agaresu ba  tare da bin hanyar da ta ba dace ba na karabar kudade.

Wadanda ake zargin dai sun karbi kudaden ne daga Bankuna da dama masu zaman kansu a daf da lokacin da za a fara zaben shekarar 2015.

sai dai dukkanin su snu musanta zargin da ake yi musu a zaman kotun.

Daga nan mai Shariah Sule Hassan ya dage cigaba da sauraranshariar har sai ranar 6 ga watan Augusta mai kamawa domin neman beli.

An daga zaman ne dai bayan jami’an hukumar zaben ta kasa mai zaman kanta sun musanta zargin da aka yi musu sannan kotun ta bayar da Umarnin da akai jami’an gidan Yari har sai ranar da za’a saurare su domin bayar da beli.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!