Labarai
Hukumar EFCC ta kama babban daraktan hukumar kula da masu kananan sana’oi
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Jihar Kwara ta kama babban daraktan hukumar kula da masu kananan masana’antu na Jihar ta Kwara Segun Soewu, kan zargin badakalar kudi naira biliyan 2.
Wata sanarwa da jami’in yada labaran hukumar Tony Orilade ya fitar a jiya Litinin, ta ce baya ga babban daraktan, hukumar ta kuma kama wasu manajojin kananan bankunan kasuwanci guda 16 bisa zarginsu da hannu a cikin almundahanar.
Wadanda aka kama din sun hadar da manajan Bankin Brightway Ogudu Samuel, da A.K. Imam Bankin Magajin gari sai Adeleke M.S. na Sincere micro Finance.
Sauran su ne Yusuf Muyiddin na Bankin Balogun Fulani Micro Finance Banka, da Isa Abdulrashid na KCMB da kuma Oyebode Asimiyu na bankin Apels.
Har ila yau akwai Lawal Ayo na bankin Omu-Aran da Tope Eniola na bankin Iludum sai Folashade Lawal ta bnkin Stockcarp da kuma Yusuf Tajuddin daga First Heritage, da kuma Olawoye E.O. na Offa Micro Finance Bank.
Toni Orilade ya ce EFCCn na zarginsu da bawa kansu bashin bankunan ba bisa kai’ida ba, kamar yadda rahoton karkashin kasa ya nuna, bayan da gwamnatin Jihar ta Kwara ta ware kudin don tallafawa kananan ‘yan kasuwa maza da mata a kananan hukumomi 16 na Jihar.