Labarai
Hukumar EFCC ta karyata ikirarin da Ayo Fayose ya yi kwanakin baya a shafin sa na Tweeter
Hukumar EFCC ta karyata ikirarin da gwamnan jihar Ekiti mai barin gado yayi kwanakin baya a shafin sa na Tweeter cewa zata dawo da shari’ar da ake wa gwaman jihar ta Ekiti Ayo Fayose.
Hakan na kunshe cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar Mr Wilson Uwujaren ya fitar a jya da daddare cewa sanarwar da gwamnan ya fitar na kamashi da za’a yi bayan ya mika milki bai fito daga hukumar ta EFCC ba.
Sanarwar wadda take a @officialEFCC da aka fitar da yammacin ranar Lahadi, hukumar ta dawo da zargin shari’ar da ake yi wa gwamnan Ayo Fayose na yin zambar Naira biliyan fiye da dubu guda.
An dai fitar da sanarwar ne bayan awanni da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar kasan sakamakon zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar Asbar a jihar ta Ekiti.