Labarai
Hukumar EFCC ta kwashe awanni 9 tana tuhumar babban hafsan sojojin Najeriya
Akalla awanni tara hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta kwashe tana tambayoyi ga tsohon babban hafsan sojin kasa na kasar nan Laftanal Janar Azubuike Ihejirika sakamakon zargin sa da almundahanar sama da naira biliyan goma sha uku.
Haka zalika hukumar ta EFCC ta kuma bukaci sanin ya akayi aka samu naira miliyan dari da goma sha biyar da dala dari da talatin da biyu da yuro dubu goma sha shida da kuma fan dubu arba’in da hudu a asusun ajiyar banki na wasu danginsa wadanda basa aikin komai.
‘Yan uwan laftanal Janar Azubuike Ihejirika da aka samu kudaden a asusun ajiyarsu ta bankin sun hada da: Raymond Ihejirika da Nkechi Ihejirika da Ndubuisi Ihejirika da Orji Ihejirika da kuma Kingsley Ihejirika.
EFCC ta kuma tuhumi laftanal Janar Azubuike Ihejirika kan sanya hannu da ya yi a takardar kwantiragin sama da naira biliyan uku da miliyan dari shida ga kamfanin wani surkinsa mai suna Chinedu Onyekwere.
Hukumar ta EFCC ta fadada bincikenta kan wasu kudade naira miliyan dari takwas da arba’in da biyar da dari shida da dala miliyan uku da dubu dari hudu da hamsin da dari shida da goma sha tara wadanda kudade ne da suka yi batan dabo a asusun kamfanin sarrafa makamai na kasa DICON.