Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar Sankarau a jihar Neja

Published

on

A kalla mutane hudu ne suka rasa rayukan su a jihar Neja sakamakon barkewar cutar sankarau.

 

Kwamishinan lafiya na jihar Dr Mustapha Jibril ne ya sanar da hakan a jiya Laraba , inda ya  ce an samu rasuwar mutanen ne a karamar hukumar Katcha da kuma Magama.

 

A cewar kwamishinan sun samun rahotanin cewar  sama da mutum 31 ne suka kamu da cutar a fadin jihar inda tara da ga ciki aka tabbatar da cutare a tare su bayan da aka yi musu gwaje-gwaje a asibiti.

 

Rahotannin na nuni da cewar annobar cutar ta sake komowa kasar nan, biyo bayan barkewar ta a wasu jihohin kasar nan a shekarar bara inda,  ta kuma janyo asarar rayukan samma da 400 wanda mafiya yawansu sun fito ne daga arewacin kasar nan.

 

Inda kuma rahotannin ke nuni da cewar jihar Zamfara ita ce jihar da tafi kowacce kamuwa da cutar.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!