Labarai
Hukumar EFCC zata daukaka kara kan batun rufe asusun gwamnatin jihar Benue
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC zata dauka ka karar kan hukuncin da babbar kotun tarayya na rufe asusun gwamnatin jihar Benue.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da mai Magana da yawon hukumar ta EFCC Tony Orilade ya fitar cewa hukuncin da mai shari’a Mobolaji Olajuwon ya yanke a babbanr kotun dake birnin Makurdi ta jihar Beneu wace gwamnatin jihar ta nemi hukumar EFCC ta biya ta kudin diyya na bata mata suna na Naira miliyan 50 da kuma wasu bankunan kasuwanci guda 2 suma su biya Naira miliyan 25.
A dai watan Agustan bara ne sashin bincike na hukumar EFCC ya bada umarnin da a rufe asusun kudi na gwamnatin jihar na wucin gadi.
Sai dai mai Magana da yawon hukumar ta EFCC ya ce lauyoyin hukumar na yi duk mai yuwa wajen daukaka kara don kalubalantar hukuncin da kotun ta yanke.