Kiwon Lafiya
Hukumar habaka harkokin kimiyya ta kasa ta ce akwai yiwuwar matsalar kutse a wannan shekara
Hukumar habaka harkokin kimiyya da fasaha ta kasa NITDA ta bukaci hukumomi da ma’aikatun gwamnati, hadi da bangarori masu zaman kan su do su yi taka tsan-tsan game da matsalar masu kutse cikin wannan shekarar.
Shugaban hukumar na kasa Dakta Isah Pantami ne ya bayyana hakan lokacin da suke zantawa da manema labarai yau a birnin tarayya Abuja.
Dakta Pantami ya kuma bayyana cewa bankuna, da ma’aikatun lafiya, bangaren bayar da hasken lantarki hadi da bangarorin samar da ababen more rayuwa, hadi da wasu bangarori daban-daban ne ake fargabar masu kutsen zasu iya yiwa danyan aiki.
A cewar sa akwai wani sashen bayar da agajin gaggawa ga wadanda suka fuskanci matsalar kutse da hukumar ta ware tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki a bangaren kimiyya, duk da nufin dakile ayyukan na su.
Shugaban hukumar ya ce yanzu haka hukumar ta daura damarar fuskantar duk wani kalubale daga bangaren masu kutsen, kuma ba zatayi kasa a gwiwa ba wajen dakile ayyukan su.