Connect with us

Labarai

Hukumar INEC ta gabatar da kasafin kusan Naira biliyan 900 na zaben 2027

Published

on

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta gabatar da kasafin kudin sama da Naira biliyan dari takwas da saba’in da uku da miliyan dari bakwai da tamanin, domin gudanar da babban zaben shekarar 2027.

Shugabannin hukumar sun bayyana cewa wannan kasafi zai taimaka wajen sayen sabbin kayan aiki na zamani, horas da ma’aikata, da kuma tabbatar da tsaro da ingancin gudanar da zaben a fadin kasar nan.

INEC ta ce karin kudin ya zama dole ne sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, fadada ayyuka, da kuma bukatar inganta fasahar tattara sakamakon zabe domin rage kura-kurai da jinkiri.

Hukumar ta kuma nemi karin kusan Naira biliyan 171 domin tafiyar da ayyukanta na shekarar 2026, wanda ya hada da shirye-shiryen tunkarar babban zaben.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!