Kiwon Lafiya
Hukumar INEC ta karyata zargin jam’iyyun siyasa na shrine daukar ma’aikatan N-Power
A wani labarin kuma Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta karyata zargin da ganayyar jam’iyyun siyasa suka yi mata na cewa tana shirin daukar ma’aikatan N-POWER a matsayin ma’aikatan wucin gadi.
Daraktan katin zabe da wayar da kan jama’a na hukumar ta INEC Mr, Oluwole Osaze-uzi bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar cewa hukumar zabe na daukar masu bautar kasa ma’aikatan wucin gadi don gudanar da zabe.
Mr, Oluwole Osaze-Uzi ya kara da cewar, sai dai in sami gibi ne, zai sanya ta yi amfani da daliban manyan makarantu, ko kuma tsofafin masu bautar kasa, amma babu wani shiri na amfani da ma’aikatan da suka ci gajiyar shirin na N-POWER.
Kuma kowa yasan cewar, tun bayan da aka kafa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na amfani da masu bautar kasa wajen gudanar da zabe a matsayin ma’aikatan wucin gadi, kuma bayar da za’a yi kwatsam wannan gwamnati ta sauya wancen tsari.