Kiwon Lafiya
Hukumar INEC ta sabunta kwamitocin da zasu kula wayar da kan, kan katin zabe
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta ce ta sabunta kwamitocin da za su riga kula da katin zabe tare da wayar da kan al’umma kan muhimmancinsa.
Kwamishinan zabe na jihar Ekiti, Ferfesa Abdul-Ganiyu ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai, jim kadan bayan sabunta kwamitocin.
Ferfesa Abdul-Ganiyu ya kuma ce, ya na da mutukar muhimmacin mambobin kwmiticin da su jajirce wajen wayar da kan al’umma kan alfanun katin zaben, duba da cewa, zaben gwamnan jihar Ekiti da na kakar zabe a shekara ta 2019 na karatowa.
Ya kuma ce, sabunta kwamitocin wani mataki ne na tabbatar da samun sahihin zabe a duk fadin kasar nan.
Daga cikin mambobin Kwamitocin da hukumar ta sabunta, sun hadar da ma’aikatun yada labarai ta kasa da ta jihar Ekiti da hukumar wayar da kan al’umma ta kasa, NOA, da ma’aikatar walwalar mata ta kasa da kuma kungiyar ‘Yan-Jaridu ta kasa.