Kiwon Lafiya
Hukumar JAMB ta ce fiye da dalibai miliyan daya ne suka yi rijista
Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB), ta ce daga fara yin rijistar jarrabawar zuwa yanzu fiye da dalibai miliyan daya da dubu dari shida ne su kayi rijistar jarrabawar ta bana a fadin kasar nan.
Mai magana da yawun hukumar Dakta Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Lagos.
Ya ce ana saran kafin nan da ranar 21 ga watan Fabrairun da aka sanya za’a rufe yin rijistar jarrabawar a fadin kasar nan, kimanin dalibai Miliyon Daya da dubu dari takwas ne za su yi rijistar jarrabawar.
Ya kuma bayyana jin dadin sa bisa yadda ake gudanar da rijistar jarrabawar a fadin kasar nan ba tare da samun wata matsala ba.
Haka kuma ya ce nan da ‘yan kwanaki hukumar za ta fara gudanar DA shirye-shiryen yin jarrabawar a cibiyoyi daban-daban da ke fadin kasar nan don ganin an gudanar da jarrabawar yadda ya kamata ba tare da samun wata matsala ba.
Benjamin ya kuma ce daliban da suka yi rijistar za su fara fitar da takardar jarrabawar ta su wato SLIP a sati biyu kafin fara gudanar da jarrabawar, don sanin ranakun yin jarrabawar da cibiyoyin da zasu rubuta jarrabawar ta bana.