Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hukumar JAMB ta ce fiye da dalibai miliyan daya ne suka yi rijista

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB), ta ce daga fara yin rijistar jarrabawar  zuwa yanzu fiye da dalibai miliyan daya da dubu dari shida ne su kayi rijistar jarrabawar ta bana a fadin kasar nan.

Mai magana da yawun hukumar Dakta Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Lagos.

Ya ce ana saran kafin nan da ranar 21 ga watan Fabrairun da aka sanya za’a rufe yin rijistar jarrabawar a fadin kasar nan, kimanin dalibai Miliyon Daya da dubu dari takwas ne za su yi rijistar jarrabawar.

Ya kuma bayyana jin dadin sa bisa yadda ake gudanar da rijistar jarrabawar a fadin kasar nan ba tare da samun wata matsala ba.

Haka kuma ya ce nan da ‘yan kwanaki hukumar za ta fara gudanar DA shirye-shiryen yin jarrabawar a cibiyoyi daban-daban da ke fadin kasar nan don ganin an gudanar da jarrabawar yadda ya kamata ba tare da samun wata matsala ba.

Benjamin ya kuma ce daliban da suka yi rijistar za su fara fitar da takardar jarrabawar ta su wato SLIP a sati biyu kafin fara gudanar da jarrabawar, don sanin ranakun yin jarrabawar da cibiyoyin da zasu rubuta jarrabawar ta bana.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!