Labarai
Hukumar jiragen kasa ta Najeriya NRC ta tabbatar da hadarin daya daga jiragen AKTS

Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da cewa ɗaya daga cikin jiragen AKTS da ke kan hanyarsa zuwa Kaduna ya yi hatsarin kufcewa daga kan layi a safiyar Talata.
A cewar hukumar, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:09 na safe, a tsakanin KM 49, dake tsakanin tashar Kubwa da tashar Asham.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata, ta ce: “Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya na tabbatar da kufcewar jirginmu na AKTS mai zuwa Kaduna daga kan layi, da misalin ƙarfe 11:09 na safe, a tsakanin KM 49 tsakanin tashar Kubwa da tashar Asham.”
You must be logged in to post a comment Login