Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rashin fahimta tsakanin ma’aurata ke jawo cin zarafi: Malam Jamilu Ibrahim

Published

on

Rikicin gida ko rikici tsakanin mata da miji abune da aka dade ana fuskanta wanda a yanzu lamarin ke ka ta’azara

Hayaniya da zagin juna, duka da cin mutunci wani lokaci ma har ta kan kai an rasa rai  sakamakon duka na faruwa tsakanin ma’aurata.

Sakamakon bincike da masa halayar dan Adam suka gudanar a lokuta daban daban na nuni da cewar anfi cin zarafin mata akan maza a fadin duniya.

Mafi yawan lokuta a nahiyar Afrika akasari da yawa maza kan yiwa mata dukan kawo wuka kan dalilin da bai kai taka kara ya karya ba , wannan dabi’a ta maza har ta kai da jefa wasu matan a wasu mataki kan dauki mataki ta hanyar ramawa da daukar makamai hakan kuwa kan  jawo mutuwar mazajen a idan tsautsayi ya gifta.

Freedom radiyo taji ra’ayoyin wasu mutane kan me ke jawowa matan ake cin zarafin su

Daga cikin su dai wata mata da ta bukaci sakaya sunanta ta bayyana cewa babban dalilin dake haddasa cin zarafin mata bai wuce sa’isa ko kuma fadi-in fada tsakanin miji da mata

Malam Jamilu Ibrahim masani ne akan halayar dan Adam dake koyarwa a jami’ar tarraya dake Dutse a jihar Jigawa ya bayyana dalilin dake jawo rikicin da cewar bai wuce idan mai karfi yayi amfani da karfin sa ba akan wanda yake kasan sa.

Shima wani malamin addini musulunci  Malam Adam Muhammad Abubakar ya bayyana illar hakan ta fuskar addini musulunci  inda ya ke cewa sabani  tsakanin ma’aurata  abu ne da ake samu sai dai ya ja hankain ma’aurata da su kasance masu yafiya da juriya tare da fahimtar juna.

Mal Adam Muhammad  ya ja hankalin ma’aurata da su san muhimmancin mutunta juna da tsare hakin kowa.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!