Labarai
Hukumar karɓar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano, ta ce za ta hukunta masu sakaci a aiki

Hukumar karɓar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano, ta ce za ta hukunta duk wani ma’aikaci da ya yi sakaci ko kin bin doka a bakin aiki.
Shugaban hukumar Comr. Sa’idu Yahaya ya bayyana haka ne yayin ziyarar ba-zata da ya kai a Asibitin Murtala Muhammad da Sakatariyar Karamar Hukumar Dala da Makarantar Aminu Kano (Legal).
Ya kuma yaba da ƙwazon ma’aikatan Asibitin Murtala, musamman a sashen haihuwa da na gaggawa, sai dai ya koka da ƙarancin manyan ma’aikata a Dala da Legal.
You must be logged in to post a comment Login