Labarai
Hukumar KAROTA na neman wani Direba Ruwa a Jallo

Kotun tafi-da-gidanka ta hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA da ke sauraron shari’ar masu karya dokokin hanya, ta ayyana wani direba mai suna Bashir Fagge, a matsayin wanda ake nema bayan ya tsere daga zaman kotu.
Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sakon murya da mai magana da yawun hukumar Abubakar Sharada ya fitar.
Kotun tafi-da-gidanka din ta KAROTA ta fara yin aiki ne a yan kwanakin nan domin hukunta masu karya dokokin hanya a Kano, sakamakon yawaitar irin wannan laifi da ke janyo asarar rayuka da dukiya.
You must be logged in to post a comment Login