Labarai
Saudiyya ta yi ragin kudin aikin Hajin bana
Hukumomi a kasar Saudiyya sun yi ragin kudin Hajji ga maniyyatan da za su sauke farali a shekarar nan ta 2024.
Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Kasa NAHCON ta sanar cewa Jalal Ahmad Arabi, ne ya nemo ragin da aka yi, wanda ya shafi kudin tikitin jirgi, masauki, jigila da sauran hidimomin da ake wa alhazai a Saudiyya.
Mai magana da yawun hukumar NACHON, Fatima Sanda Usara ce ta sanar da hakan a ranar Laraba.
Wacce ta ce ‘a sakamakon haka, Saudiyya ta rage “Dala 138 daga kudin tikitin jirgin da aka biya a 2023, masauki a Madina daga Riyal daga 2,080 ya koma 1,665, masauki a Makkah ya koma Riyal 3,000 daga 3,500.
“Zama a Muna da Arafa da Muzdalifa kuma an rage shi zuwa Riyal 5,393 zuwa 4,770,” in ji ta.
Kazalika ana hasashen duk da wannan saukin da Saudiyya ta yi, da wuya maniyyayatan Najeriya su shaida sauƙin daga Naira miliyan 3 da suka biya a 2023 sakamakon tashin farashin Dala.
Akasari ana biyan kudin aikin Hajji da sauran huldodin kasa da kasa, kamar aikin Hajji da sauransu ne da Dala ko sauran kudaden kasashen waje.
Faduwar darajar kudin Najeriya, Naira da tashin dala da danginsa a kasar ta sa a duk shekara kudin aikin Hajji karuwa.
A sakamakon haka ne aka samu karin kashi 50 a kudin aikin Hajjin 2024 a kan na 2023.
Rahotanni sun bayyana cewa an samu raguwar maniyyayatan Najeriya da za su sauke farali a bana a sakamakon tsadar kudin kujera.
You must be logged in to post a comment Login