Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kasuwannin canjin kudade a Nijeriya sun fara yajin aiki

Published

on

A yammacin jiya Laraba ne kasuwar musayar kudade ta WAPA da ke Kano, ta ce ta rufe na wasu sa’o’i a daidai lokacin da farashin dala daya ya haura naira 1,500.

Sakataren Kasuwar Canjin Kudi ta WAPA a Kano Haruna Musa Halo ya ce “sun rufe kasuwar ne sakamakon kiraye-kirayen da DSS da EFCC suke yi musu”.

Sai dai Sakataren ya ce “a yau Alhamis 1 ga watan Fabraru ne da karfe 12:00 na rana ne za su koma aiki da zarar lamura sun daidaita”.

Itama dai Kungiyar ‘yan kasuwar canji ta Birnin Tarayya Abuja ta ce daga yau Alhamis din ne 1 ga watan Fabraru ne za ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani sakamakon tsadar dala da ke ake fama da ita a Najeriya.

Shugaban kungiyar, Alhaji Abdullahi Dauran shi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

Ya alakanta tashin gwaron zabi da Dalar ta yi da ayyukan kamfanin hada-hadar kudade ta Intanet na Crypto da ake kira Binance.

Darajar takardar kudin Nairar dai ta yi faduwar da ba ta taba yi ba cikin gomman shekaru a tarihin Najeriya.

Bayan cece-kucen da al’ummar Kasar suke Yi ne ya sanya Majalisar Dattawa ta gayyaci Gwamnan CBN kan faduwar darajar naira.

A cewarsa, “hukumomin na ƙoƙarin jin ba’asin da ya sanya Dalar ke ci gaba da tashi kusan kullum, lamarin da ya jefa tattalin arzikin kasar cikin tsaka mai wuya.

A hannu guda Kuma, Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS da Hukumar Yaƙi da cin hanci da Rashawa ta EFCC sun soma bincike domin gano dalilin tashin gwaron zabi da dala ta yi a kasuwar musayar kuɗi a kasar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!