Kiwon Lafiya
Hukumar kiyayye auhadura ta kasa ta tabbatar da rasuwar sanata John Shagaya
A jiya Lahadi ne Hukumar kiyayye auhadura ta kasa ta fayyace a hukumance yadda tsohun sanata John Shagaya daga jihar Filato ya mutu a sakamakon hatsarin mota a ranar Lahadi.
Mai Magana da yawun hukumar Bisi Kazeem a cikin wata sanarwar da ya fitar ya ce bayan da hukumar ta gudanar da bincike Mr Shagaya na kan hanyar sa ne na zuwa Lantanga zuwa Panskshin wadda bababbar hanya ce zuwa garin Jos, yayin da motar sa ta bugi wata turmujejiyar bishiya gamu da hatsarin a dai-dai karfe 2 da minti 25 na ranar.
Shi dai marigayi Mr Shagaya ya samu mumunan rauni a akan shi a yayin hatsarin kuma ya mutu nan take, kuma tuni aka kai gawar sad akin ajiye gawawaki na rundunar sojan kasar nan dake Jos babban birnin jihar ta Fialato.
Bayanan sun yi kamanceceniya da wanda al’umma suka ji a kafafan yada labarai bayan da ahatsarin ya afko.
A cewar, Bisi Kazeem Mr Sahagaya wanda birgediya Janaral ne mai ritaya na cikin wata mota kirar Toyota Land Cruser SUV na tare da direban sa da kuma dogarin sa, wanda jami’in hukumar civil defence ne, a yayin da suka gamu da mumunan hadarin.