Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3

Published

on

Hukumar dakile da abkuwar hadurra ta kasa (FRSC) shiyyar jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon fadawa da motar da suke tafiya a ciki ta yi, a cikin wani kogi da ke jihar Bauchi.

A cewar hukumar ta FRSC, mutanen uku sun yi hatsarin ne a ranar goma sha biyu ga wannan wata da muke ciki na Maris amma ba a kai ga gano su ba, sai bayan kwanaki uku.

Hatsarin dai ya abku ne a garin Tasham Turmi da ke da nisan kilomita uku akan hanyar Bara zuwa Gombe a yankin karamar hukumar Alkaleri.

Kwamandan hukumar dakile abkuwar hadurra ta kasar a jihar Bauchi Yusuf Abdullahi shi ya bayyana hakan ga manema labarai a Bauchi.

A cewar hukumar, duk mutane ukun da ke cikin motar wadanda maza ne sun rasa rayukansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!