Labarai
Hukumar NAHCON zata bude kwalejin yin bita ga maniyyata
Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON tace ta tura takardar neman yardar bude kwalejin da za’a rinka bitar Mahajata, ga Hukumar kula da Makarantun koyar da sana’o’i ta kasa.
Shugaban hukumar ta Kasa NAHCON Alhaji Kunle Hassan ya bayyana hakan yayin karanta takardar dake kunshe da neman izinin bude kwalejin ga shugaban Hukumar kula da Makarantun koyar da sana’o’i Dr. Mas’udu Adamu Kazaure a Jihar Kaduna a Jiya.
Alhaji Kulle Hassan yace bude wannan Kwalejin zai taimaka wajen wayar da kan Mahajjata, tare dayi musu bita kan yadda aikin Hajji yake gudana, kana ma’aikatar zata wallafa fefen bidiyo, da kuma littafi da za’a rinka siyarwa, mai dauke da yadda aikin Hajji ke gudana.
A bangaren shugaban Hukumar kula da makarantun koyar da sana’o’i Dr. Mas’udu Adamu Kazure kuwa, yabawa shugaban NAHCON din yayi, dangane da wannan yunkurin nasa, wanda zai taimaka wajen habaka arzikin kasar nan.
Dr. Mas’udu yayi alkawarin tura jami’an ma’aikatar tasu zuwa hukumar a sati mai kamawa, don fara shirye-shiryen da suka kamata.
SFB
You must be logged in to post a comment Login