Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu ta rufe wani asibiti a Kano

Published

on

Hukumar dake kula da asibitoci masu zaman kansu a jihar Kano PHIMA ta kara rufe wani asibiti, tare da rufe dakunan fidar wasu asibitoci uku a wasu kananan hukumomin jihar nan.

Hukumar PHIMA ta bakin shugaban gudanarwa Isa Isyaku yace sun kai samamen wadannan asibitoci ne sakamakon rashin bin ka’aidar daukar kwararrun ma’aikata, da rashin ingancin dakunan fida, da kuma kin yin rajistar da hukumar su.

Yayin samamen hukumar ta rufe wani asibiti mai suna Kabir Global Clinic dake garin Rimi a karamar hukumar Sumaila, sai kuma rufe dakunan fidar asibitocin Habeeba Salam Clinic a karamar hukumar Garko, da Gidan ruwa clinic a karamar hukumar Wudil da kuma Ali Alkali Clinic dake karamar hukumar Takai.

Asibitin Kabir Global zai ci gaba da zama a rufe, da kuma dakunan fidar sauran asibitocin har sai hukumar ta gama binciken ta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!