Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Gwamnatin Kano zata sayar da bankunan kasuwancin ta guda 30

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ce kofar ta a bude take ga duk masu San siyan hannun jarin bankunan ta na Bunkasa masana’antu wato Microfinance Bank.

Shugaban Kwamitin da Gwamnatin ta kafa dan siyar da bankunan Kuma tsohon kwashinan Kudi na Jihar Kano, Dakta Aminu Mukhtar Dan’amu shi ne ya bayyana haka a yayin taron tattaunawa da wasu daga cikin ‘Yan kasuwa da kuma kamfanoni.

Dakta Aminu ya ce gwamnatin ta tallata wadannan Bankuna guda 30 dan siyar dasu baki daya a bisa dokar Babban Bankin kasa na CBN na cewa a siyar da bankunan kasancewar gwamnati bata rike banki.

Shugaban ya Kuma ce bawai iya ‘Yan kasuwar Jihar Kano bane, suke da damar siyan bankunan ba, hatta sauran ‘yan kasuwa daga wajen Jihar Kano suna damar siyan bankunan na microfinance.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!