Kiwon Lafiya
Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sammaci babban sakataren a ma’aikatar lantarki ayyuka da gidaje
Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta kasa ta yi sammacin babban Sakatare a ma’aikatar Lantarki ayyuka da gidaje Mista Louis Edozien domin gurfana gabanta tare da amsa tambayoyi almundahana.
Rahotanni sun bayyana cewa cewa Mista Louis Edozien zai gurfana a Sakatariyar hukumar da ke birnin tarayya Abuja a yau Laraba.
Gayyatar dai ta biyo bayan takardar korafi da wata tsohuwar babbar Manajar kamfanin samar da wutar lantarki na Neja-Delta Maryam Muhammad ta rubatawa hukumar ana zargin babban Sakataren da rashincancantar mukamin na sa, baya ga son rai da ya rika sanyawa cikin aikin.
Mista Edozien wanda shi ma ya taba rike mukamin babban manajan kamfanin samar da lantarkin na Neja-Delta, ya zamanto cikin manyan Sakatarori 18 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a cikin wtan Nuwamban shekarar 2015.
Maryam Muhammad ta shaidawa hukumar kula da da’ar ma’aikatan cewa a baya can an kori Mista Louis Edodien daga aiki a kamfanin sakamakon gaza gabatar da ingantacciyar shaidar aikin bautar kasa wato NYSC ceritificate, bayan dogon bincike.