Labarai
Hukumar kula da harkokin ƴan sanda ta ƙasa ta ki ƙarawa Ibrahim Magu muƙami
Hukumar kula da harkokin ƴan sanda ta ƙasa PSC ta ki amincewa ta yiwa tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC Ibrahim Magu.
A yau alhamis ne hukumar ta PSC ta yiwa wasu manyan jami’an ƴan sanda ƙarin girma.
Hukumar kula da harkokin ƴan sanda ta Njeriyar ta ce ba za yiwa Ibrahim Magu ƙarin girma ba, har sai ta samu umarnin hakan daga ofishin atoni janar na ƙasa Abubakar Malami.
A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani wanda kuma aka rabawa manema labarai a yau alhamis, ta ce, da zaran an samu takardar da ta wanke Ibrahim Magu daga ofishin atoni janar na tarayya to kuwa za a ƙara masa girma.
Abaya-bayan nan ne rahotanni suka bayyana cewa akwai alamar ƙarin girma ga Ibrahim Magu duk kuwa da zargin da ake yi masa na badaƙala lokacin yana jagorancin hukumar EFCC.
Cikin waɗanda hukumar ta yiwa ƙarin girma akwai manyan mataimakan sufeta janar-janar na ƴan sanda guda uku da kuma kwamishinonin ƴan sanda guda ashirin da huɗu waɗanda aka yiwa ƙarin girma zuwa muƙamin sufeta janar na yan sanda.
A ɓangare guda hukumar ta PSC ta kuma yiwa manyan mataimakan kwamishinan ƴan sanda guda talatin da biyar ƙarin girma zuwa muƙamin kwamishinonin ƴan sanda, yayin da mataimakan kwamishina hamsin da biyu aka ɗaga likkafarsu zuwa manyan mataimakan kwamishina sai kuma manyan sufirtanda guda arba’in da shida da aka ƙara musu girma zuwa muƙamin mataimakan kwamishinan ƴan sanda.
Sabbin manyan mataimakan sufeta janar na ƴan sandan sun haɗa da: Tijjani Baba wanda ya maye gurbin DIG Aminchi Sama’ila Baraya d aya yi murabus a baya-bayan nan daga yankin arewa ,maso gabas sai Zanna Muhammed Ibrahim shima daga yankin arewa maso gabas da ya maye gurbin DIG Ibrahim Lamurde mai ritaya sai kuma DIG Moses A Jitoboh wanda ya maye gurbin DIG Ogbizi Michael da ya yi ritaya a baya-bayan nan daga yankin kudu maso kudu.
Da ya ke jawabi bayan sanar da ƙarin girma ga sabbin ƴan sandan shugaban hukumar kula da harkokin ƴan sanda ta kasa Alhaji Muslimu Smith ya hore su da su zage dantse wajen ba da gudumawarsu don daƙile matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan a wannan lokaci.
Sannan ya buƙace su da su guji duk wani abu da zai zubar da ƙimar rundunar ƴan sandan ƙasar nan
You must be logged in to post a comment Login