Kiwon Lafiya
Hukumar kula da sararin samaniya ta musanta matsalar yanayi da dage zabe da hukumar INEC ta yi
Hukumar da ke kula da sararin samaniyar kasar nan NAMA ta zargi hukumar zabe ta kasa INEC da fakewa da matsalar yanayi wajen dage zabe, inda ta ce ko kadan babu wata matsalar yanayi da aka samu a ranar juma’ar da ta gabata da ta hana jirage zirga-zirga.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Lahadi da ke dauke da sa hannun jami’in yada labaran hukumar Khalid Emele.
Ta cikin sanarwar hukumar ta NAMA ta zargi hukumar ta INEC da fakewa da matsalar yanayi, wajen kawo uzurin dage zabe, inda hukumar ta ce bata da wani matsalar yanayin sararin samaniya da zai hana jirage tashi.
Ya kuma ce hukumar ta yi aiki a daren juma’ar da ta gabata na tsahon awanni 24 domin tabbatar da cewa ta yi safarar kayayyakin zaben zuwa sassan kasar nan baki day aba tare da samun wata matsala ba.
Ya kuma ce har kawo yanzu hukumar ba ta da wata matsala da za ta hana ko dakile wani jirgin sama tashi a dukkanin filin jiragen saman kasar nan.