Connect with us

Kiwon Lafiya

kungiyar ta NLC ta bukaci hukumar INEC ta tabbatar da an gudanar da sahihin zabe a jihohi 6 da ba’a kammala ba

Published

on

Kungiyar ma’aikatan kwadago ta kasa NLC ta bukaci hukumar zabe ta kasa INEC  da ta tabbatar da an gudanar da sahihin zabe a jihohi shida da ba’a kammala zaben su ba a sassan kasar nan.

Haka kuma kungiyar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sake duba rahoton da kwamitin mai shari’a Muhmmadu Uwais suka mika masa kan sake yiwa dokokin zaben kasar nan kwaskwarima wajen shawo kan matsalolin da aka fuskanta a zaben bana.

 Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai rikon shugabancin kungiyar Amechi Asugwni ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Abuja.

Kungiyar ta kuma nuna takaicin ta na dage zabukan kasar nan da hukumar INEC ta yi bayan da ta tsara cewa za’a gudanar da shi a ranar 16 ga watan na jiya zuwa ranar 2 ga watan Maris tun da fari, tare da rashin kammala hada sakamaon zaben akan lokaci inda tace hakan na iya kawo tarnaki wajen cigaban dumokuradiyya

Haka kuma kungiyar ta yabawa hukumar zaben dangane da amfani da naurar Card Reader da takeyi a yayin zabukan da suka gudana a kasar nan, duk da matsalolin da aka fuskanta

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,747 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!