Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Hukumar kwallon kafa ta Ingila tace ba zata laminci cin zarafin ‘yan wasa ba

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta kasar Ingila tayi All… wadai da cin zarafin wasu ‘yan wasan kasar biyo bayan rashin nasara kan Italiya a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020.

Yayin da kasashen suka yi kunnen doki da ci 1-1, hakan ne ya sanya zuwa bugun daga kai sai mai tsaro raga a wasan da aka gudanar ranar Lahadi 11 ga watan Yulin 2021.

Kasar Italiya dai ta doke Ingila da ci 3-2, inda ‘yan wasa Marcus Rashford da Jadon Sancho da kuma Bukayo Saka suka zubar wa da kasar Ingila.

Sakamakon haka ne wasu daga cikin magoya bayan kasar ta Ingila ke ganin beken ‘yan wasan uku kasancewarsu bakake.

Hukumar ta ce, “Munyi mamaki da ake nuna wa wasu ‘yan wasanmu wariyar launin fata, a don haka ba za mu yadda da duk wani nau’in nuna wariya ba.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!