Labarai
Hukumar NAHCON ta kafa kwamitoci don shirye-shiryen aikin Hajjin 2019
Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta kafa wasu kwamitoci guda uku domin shirye-shiryen aikin Hajjin badi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Fatima Usara.
Sanarwar ta ruwaito cewa shugaban hukumar Abdullahi Muhammed ne ya kaddamar da kwamitocin a birnin Makkah a jiya Lahadi.
A cewar sanarwar, mambobin kwamitocin guda uku sun kunshi: jami’an hukumar ta NAHCON da kuma jami’an hukumar jin dadin alhazai na jihohi; kuma za su yi aiki ne wajen neman masaukan alhazai da sauran wasu lamuran na daban a biranen Makkah da Madina.
Shugaban hukumar ta NAHCON ta cikin sanarwar ya kuma ya bawa halayyar alhazan kasar nan a kasa mai tsarki; yana mai cewa, ya zuwa yanzu; alhazai dubu goma sha biyu ne aka dawo da su gida ta cikin jigila arba’in da jirage su ka yi.