Kiwon Lafiya
Hukumar Naptip ta kama wasu mutane 8 da zargin safarar mutane
Hukumar yaki da safarar mutane ta kasa NAPTIP ta ce ta kama wasu mutane takwas da ake zargin masu safarar mutane ne.
Shugaban hukumar da ke kula da shiyyar garin Benin Mista Nduka Nwanwenne shi ne ya shaidawa manema labarai hakan a yau Laraba a garin Benin da ke jihar Edo inda ya ce an kama wadanda ake zargin ne watanni uku da suka gabata.
A cewar sa hukumar ta kubutar da akalla mutane 138 da aka yi safarar su a tsakanin lokacin da aka kama su inda kuma wasu 124 daga cikin wadanda aka kubutar suka koma ga dangin su.
Shugaban ya kuma ce kawo yan zu batutuwan harkar safarar mutane da ke gaban kotuna daban daban a kasar nan sun kai tamanin da tara.
Ya kuma ce sun samu rahotannin safarar mutane har 34 daga korafin da ake aikewa hukumar daga dai-daikun mutane, inda kuma ta samu rahoton wasu goma sha hudu daga hannun jami’an tsaro.