Kiwon Lafiya
Hukumar NCDC ta tabbatar da mutuwar mutane 166 sakamakon cutar Lassa

Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC, ta tabbatar da mutuwar mutane 166 sakamakon cutar Lassa daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 14 ga watan Satumban bana.
Rahoton da NCDC ta fitar, ya nuna cewa cutar ta Lassa ta ci gaba da addabar wasu jihohi inda aka ruwaito sabbin kamuwa da cutar a lokuta daban-daban.
Hukumar ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da kiyaye dokokin tsafta, da yin amfani da abinci da aka rufe sosai, tare da guje wa hulɗa da beraye, wadanda ake ganin su ne manyan hanyoyin yada wannan cuta.
You must be logged in to post a comment Login