Labarai
Mun kama masu safarar kwayoyi 19 a Filin Jirgi na Kano a 2025- NDLEA

Hukumar Hana Sha da Safarar Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, reshen Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, ta ce daga farkon shekarar 2025 zuwa yanzu ta kama mutane 19 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.
Kwamandan NDLEA mai kula da Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa a Kano, Adamu Karami, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da Freedom Rediyo.
Hukumar ta bayyana cewa daga cikin waɗanda aka kama akwai wata mace ’yar ƙasar Indiya, wadda ake zargin ta da safarar hodar iblis mai nauyin kilogram 11, adadin da ya fi kowanne yawa da aka taɓa kama a tarihin Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.
You must be logged in to post a comment Login