Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar NDLEA ta kama wani mutum da ake zargin da safaran makamai jihar Benue

Published

on

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wani mutum da ake zargi da Safaran Bindigogi zuwa Jihar Benue.

Mataimakin kwamandan hukumar a Jihar Jigawa Oko Michael ne ya tabbatar da hakan yana mai cewa jami’ansu ne suka kama mutumin a ranar Lahadin da ta gabata a yayin da su ke aikin sintiri a kan hanyar Jahun zuwa Gujungu.

Mutumin mai suna Salisu Mamuda da suka ce dan asalin Jihar Kaduna ne, ya yi karatunsa ne a Jihar Nassarawa inda kuma ya ke aikin safarar karafunan da suka lalace daga Jihar ta Nassarawa zuwa Benue.

Salisu Mamuda, ya ce wasu mutane daga Jihar Benue ne suka bukaci ya kai musu Bindigogin ta hanyar amfani da wani abokinsa.

Hukumar ta NDLEA ta ce za ta mika mutumin tare makaman da aka samu a hannunsa zuwa hannun ‘yan-sanda a Jihar ta Jigawa domin fadada bincike.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,401 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!