Labarai
Hukumar NERC zata soke lasisin kamfanonin raba wutar lantarki
Hukumar da ke kula da al’amuran wutar lantarki ta kasa NERC ta bayyana kudirinta na soke lasisin wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki wato DisCos nan da kwanakin 60, sakamakon bashin kimanin fiye da biliyan 30 na kudaden lantarki da ake bin su.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannu shugaban hukumar ta NERC Dafe Akpeneye ya bayyanawa manema cewar hukumar da ke lura da al’amuran lantarki ta bukaci babban birnin tarayya Abuja da jihohin Benin da Enugu da Ikeja a jihar Lagos da Kano da Kaduna da birnin Fatakwal da Yola , su gabatar da dalilan da ya sanya ba za’a soke lasisin su ba nan da wata biyu, masu zuwa.
Hukumar ta bayyana cewa muddin kamfanonin rarraba wutar lantarkin ta kasa, suka gaza hada kudaden da ake bin su, ga kamfanin da ke tattara kudaden wutar lantarki za’a soke lasisinsu.
Kamfanin TCN ya ce wasu kwantenoninsa guda biyu sun yi batan dabo
Hukumar NERC ta ce tana bin kamfanin rarraba wutar lantarki fiye da naira biliyan 36 na wutar lantarki da aka basu a watan Yulin da ta gabata har kawo yanzu suka gaza biya .
Kamfanin DisCos din dai sun biya fiye da naira biliyan 5 wanda a yanzu haka ake binsu kimanin biliyan 30.
Rahotanin sun bayyana cewar, wannan shi ne karo na farko da zata fara amfani da dokokin na biyan kaso 100 na lantarkin da aka aike mata.
Rashin biya wadannan kudade dai ka iya tunzura hukumar NERC wajen soke lasisin wadannan kamfanoni.