Addini
Hukumar Shari’a ta Kano ta ce ta Samar da kalandar Muslunci ta shekarar nan guda dubu 20
Hukumar Shara’a ta jihar kano ta ce gwamnatin jihar Kano ta samar da sabuwar kalandar Muslunci ta wannan shekarar sama da dubu Asirin domin rabawa ga al’ummar jihar da masallatai da sauran bangarori da suka shafi addinin musulunci
Mukaddashin hukumar Shara’ar na Kano Dakta Gwani Yusha’u Abdullahi Bichi ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai kan yadda gwamnatin kano take yunkuri wajen samar da duk wani abu da ya dace ga wannan hukumar domin ƙara martabar hukumar.
Ka zalika Gwani Yusha’u ya ce hukumar shara’a ta jihar Kano tana gudanar da ayyukan ta da suka haɗar da shiga yankuna domin musuluntar da al’umma da kuma sasanci ga dukkan abin da ya shafi addini musamman harkar Aure da jagorancin musabaƙa da gwamnati ke yi.
Haka kuma yace za’a suna yabawa da yadda wannan gwamnatin ta tsaya wajen ganin an samarwa da wannan hukuma duk wani abu da take muƙata musamman harkar kalandar Muslunci
You must be logged in to post a comment Login