Labarai
Hukumar Shari’a ta ziyarci Babbar Jojin Kano Dije Abdu Aboki

Hukumar Shari’a ta jihar Kano ta kai ziyara ofishin Babbar Jojin jiha, Mai shari’a Dije Abdu Aboki domin kulla alakar aiki.
Shugaban Hukumar Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya jagoranci shugabanni da Ma’aikatan zuwa Sakatariyar Audu Bako domin ganawa da ita.
Sheikh Daneji ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin taya ta murna tare da neman hadin kai da Hukumar ta Shari’a wajen inganta ayyukan da suke gudanarwa.
Daneji ya ce, hukumar tasu ta na bukatar karin Lauyoyi musamman a duk lokacin da suka samu wata kara da za a shiga tsakani.
A jawabinta, babbar jojin jihar Kano mai shari’a Dije Abdu Aboki, ta bayyana jin dadinta bisa wannan ziyara, tare da bada tabbacin bayar da gudummawa ga hukumar ta shari’a a dukkanin bangarorin da ta ke da hurumi a kai.
A yayin ziyarar Sheikh Abbas Daneji na tare da Kwamishina na 1 a ma’aikatar shari’a Gwani Hadi da kuma kwamishina na 2 Sheikh Ali Danabba da sauran Mambobi da Daraktocin ma’aikatar.
You must be logged in to post a comment Login