Labarai
Hukumar tara kudaden shiga ta sanya kimanin tiriliyan 4 a asusun gwamnati
Hukumar tara kudaden shiga ta kasa FIRS ta ce ta sanya kimanin tiriliyan 4 da biliyan 63 a asusun gwamnatin tarayya daga farkon watan Janairu zuwa watan nuwambar shekarar nan da muke bankwana da ita a yau.
Wannan na kunshe cikin kundin bayanin harajin da kasar nan ta samu a shekarar da muke bakwana da ita da kwamitin rabon tattalin arzikin kasa ya gabatar cikin satin daya gabata.
Wannan adadi dai ya nuna hukumar ta FRSC ta samar da kusan kaso 72 cikin abinda aka yi hasashen zata samar a wannan shekara cikin kasafin kudin bana.
Kwamitin rabon tattalin arzikin kasar wanda minister kudi Zainab Ahmad ke jagor anta ya kunshi kwamishinonin kudin jihohin kasar nan 36 da kuma akanta janar na kasa Ahmad Idris.
Ragowar mambin kwanitin sun hadar da wakilai da ga hukumomin da ke Tarawa kasa haraji da suka hadar da kamfanin main a kasa NNPC da hukumar kwastam sai kuma sahin kula dararraba man fetur na kasa DPR.
Sauran sun hadar da babban bankin kasa CBN sai kuma hukumar kiyaye hadura ta kasa FRSC sau kuma NEITI da sauran su.